Header Ads

Sabuwar Naira: Gwamnatin jihar Jigawa ta koka kan karancin sabbin kudi

Gwamnan jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta koka kan karancin sabuwar naira, inda ta bayyana cewa mutane a jihar na kwana a layin na'urar cire kudi ta ATM.

Kwamishinan kudi da cigaban tattalin arzuki na jihar, Babangida Gantsa, ne ya bayyana haka a ranar Laraba bayan ya kai ziyara bankuna daban-daban a jihar, inda ake samun kusan mutum 250 a kan layin cire kudi a banki.

Kwamishinan ya bayyana cewa, rashin isassun kudaden a hannun mutane ya gurgunta al'amuran da suka shafi tattalin arziki a jihar, inda ya ce mutane na kwana a layin na'urar cire kudi a bankuna.

Kwamishinan ya kara da cewa, halin da jama'a suka shiga ya sa gwamnan jihar ya umarce shi da ya zagaya bankunan da ke birnin jihar, kuma manajojin bankunan sun shaida masa cewa babban bankin Nijeriya bai ba su isassun kudin da za su sawa na'urar cire kudi ta ATM ba.

"Akwai na'urar cire kudi da na kirga mutane 215 suna kan layin cire kudi, akwai wadda mutane sama da 250 ke bin layi domin cire kudi, an ce mafi yawansu sun kwana a nan.

"Wannan matsala ta yi lahani ga kasuwanci domin rashin sabbin kudade a jihar." Kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.