Header Ads

Wani ya rasa ransa a yakin neman zaben APC a jihar Bauchi

Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a jihar Bauchi, Air Marshal Sadique Baba Abubakar

Mutum daya ya rasa ran sa, a yayin da wani kuma ya jikkata, a wani yakin neman zaben jam'iyyar APC a jihar Bauchi.

Yadda lamarin ya faru kuwa, kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya shaida wa 'yan jarida shi ne, "A ranar Litinin da karfe 8:30 na dare dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, a lokacin da yake kan hanyarsa daga Dambam zuwa Akuyam domin yakin neman zabe, gab da shigar su Akuyam an kai farmaki ga tawagarsa."

Kamar yadda ya bayyana, bayan kai wa tawagar farmaki ne, sai wani daga cikin matsara na tawagar dan takarar ya bude wuta har ya samu mutum biyu, Saleh Garba dan shekara 35, da Yakubu Yunusa dan shekara 20, dukkanin su mazauna kauyen Akuyam, kuma dukkaninsu an tafi da su asibitin FMC da ke Azare domin samun kulawar likitoci.

To sai dai kamar yadda ya bayyana, a ranar Talata ne aka samu tabbacin rasuwar daya daga cikin mutanen a yayin da yake samun kulawar likitoci, kuma tuni kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Bauchi, Aminu Alhassan, ya bayar da umarnin a kaddamar da bincike cikin al'amarin, ya kuma yi addu'ar samun rahama ga wanda ya rasu cikin mutanen biyu.

A ranar 24 ga watan Nuwambar 2022 ne dai kwamishinan 'yan sandan ya gana da jam'iyyun siyasa a jihar, inda ya nemi da su gudanar da harkokin siyasarsu bisa kan ka'ida tare da bin dokokin zabe da kuma bukatar su da su yi siyasa ba da gaba ba.

Da yake magana da 'yan jaridu a kan lamarin, daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam'iyyar ta APC a Bauchi, Alhaji Salisu Barau, ya ce duk da harin da aka kawo masu, amma sun hana magoya bayansu mayar da martani domin kare rayuka da dukiya.

No comments

Powered by Blogger.