Header Ads

An rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban Nijeriya, yayin da mulkin Buhari ya zo ƙarshe

Sabon shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a dandalin Eagle Square da ke Abuja a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Bayan gudanar da al'amurra da dama da suka shafi zabe na tsawon watanni, Nijeriya ta samu sabon shugaban kasa wanda zai kula da al'amurran ta na tsawon shekaru hudu masu zuwa, wannan shugaba kuwa shine Bola Ahmed Tinubu, dan shekaru 71.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne, an rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Nijeriya na 16 a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun shekarar 2023 a dandalin Eagle Square da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Babban alkalin Nijeriya, Alkali Olukayode Ariwoola, ne ya karanto rantsuwar shiga ofishin shugaban kasar ga Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da misalin daidai karfe 10:28 na safe da kuma misalin daidai karfe 10:38 na safe. 

Sojojin kasa na Nijeriya sun gudanar da fareti cikin kaya na musamman bayan rantsuwar da kuma bikin rantsuwar wanda Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan suka halarta. 

Matar Tinubu; Remi, matar Shettima; Nana da kuma matar Buhari; Aisha duk sun halarci bikin rantsuwar da aka yi.

Wasu shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron kuma wadanda suka halarci bikin sun hada da sabon Firaministan kasar Gabon, Billy By-Nze, shugaban kasar Jamhuriyar Cote D'Ivoire, Alassane Ouattara; shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo; da shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame.

Akwai dai wasu manyan baki a wurin taron wadanda suka hada da Akinwumi Adesina, Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdulsamad Rabiu da Jim Ovia.

Saura wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin hukumomin tsaro, gwamnoni, tsofaffin gwamnoni, ministoci na yanzu da tsofaffi da kuma shugabannin jam'iyyar APC.

Yayin da ake fuskantar hauhawar rashin aikin yi, tsadar kayayyaki, tabarbarewar tsaro da sauransu a Nijeriya, sama da mutane miliyan 200 na bukatar ganin abubuwa da dama daga shugaban kasa Tinubu.

Yayin da ya ke jawabi a wajen rantsarwar, Tinubu ya sha alwashin kawar da ta'addanci da aikata laifuffuka daga Nijeriya. 

Sabon shugaban kasar ya yi alkawarin gyara tattalin arzuki kasa. Shugaban ya bayyana cewa zai kawo karshen talauci, zai samar da isasshen abinci, tabbatar da cewa ana tafiya tare da mata da matasa da kawo karshen cin hanci. 

Tinubu, wanda kamfe din sa ya dogara a kan abubuwan da ya ke son yi masu shafuka 80 wadanda ke yin nuni da ajandoji guda 8, ya yi alkawarin zai yi adalci ga duka 'yan Nijeriya.

No comments

Powered by Blogger.