El-Rufai ya soke wata ƙungiya da ke kudancin Kaduna 'yan awowi kafin ya miƙa mulki
'Yan awowi kafin ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ta bayyana kungiyar Atyap Community Development Association a matsayin kungiyar da ba kan doka ta ke ba tare da sa hannu domin soke ta.
Umarnin soke kungiyar ya ya yi ikirarin cewa kungiyar ta kudancin Kaduna ta shiga cikin ayyukan da za su iya lalata zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman tare da kyakkyawan mulki a jihar.
A wani jawabi ta bakin kakakin El-Rufai, Muyiwa Adekeke, ya bayyana cewa gwamnan ya sa hannu a umarnin (soke) Atyap Community Development Association, 2023 a karkashin ikon da ya ke da shi wanda sashen na 60 na dokar Kaduna State Panel Code mai namba ta 5 na shekarar 2017 da kuma sashe na 5 (2) na tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya ya ba shi.
Umarnin sokewar zai fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2023.
Umarnin sokewar ya nuna cewa sashe na 38 da 40 na tsarin mulkin tarayyar Nijeriya ya tabbatar da 'yancin tunani, lamiri da addini da kuma 'yan cin yin kungiya da taron zaman lafiya ga duka 'yan kasa.
Post a Comment