Ƙasashen Turai 10 sun yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da rusa gidajen Falasɗinawa
Kasashen turai 10 sun yi kira ga Isra'ila da ta dakata da tsarin ta na rusa gidaje da kwace kadarorin Falasdinawa a yamma da gabar Kogin Jordan da aka mamaye.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency (TNA) ta ruwaito, kiran na zuwa ne a cikin wani jawabi na hadaka da ofisoshin kasashen Belgium, Faransa, Italiya, Andalusia (Spain), Sweden, Ingila, Denmark, Finland, Jamus, Ireland da kuma ofishin wakilan majalisar kasashen turai a yamma da gabar kogin Jordan da Gaza.
Jawabin ya yi kira ga "Isra'ila, gwamnatin mamaya, da ta dakatar da duk kwace-kwace da rushe-rushe ta kuma samar da dama ba tare da hanawa ba ga kungiyoyi masu aikin jin kai a yankin yamma da gabar kogin Jordan ciki har da gabashin Jerusalem."
A cikin jawabin sun ma nemi Tel Aviv "Da ta maido ko ta biya diyyar duk wasu kayayyaki da kungiyoyin masu aikin agaji suka samar." Wannan na nufin rusa gine-ginen da majalisar kasashen turai ta gina tun shekarar 2015 wanda kudinsu ya kai Euro 1,291,000 (dalar Amurka 1,385,300).
Kasashen guda 10 "Da kakkausar murya sun yi Allah wadai da rushe makarantar da masu aikin agaji suka gina a Jubbet Adh Dhib." Inda suka nuna "matukar damuwarsu a kan barazanar rushe wasu makarantu guda 57 a yamma da gabar kogin Jordan."
Domin boye manufarta, Isra'ila kan yi amfani da hujjar rashin umarnin gini domin rushe gidajen Falasdinawa, musamman wadanda ke Area C wadda ke karkashin ikon sojojin Isra'ila.
Kamar yadda ya ke a cikin yarjejeniyar shekarar 1995 ta Oslo Accord a tsakanin Isra'ila da kungiyar samar da 'yanci ga Falasdinawa (PLO), yamma da gabar kogin Jordan, ciki harda gabashin Jerusalem, an raba su ne kashi uku - Area A, B da C.
Post a Comment