Header Ads

Masu fafutikar kafa ƙasar Yoruba ƙarƙashin jagorancin "Black Lion" sun yi yunkurin kwace iko da wani gidan rediyon gwamnatin tarayya


Wasu masu fafutikar kafa kasar Yoruba

Wasu masu fafutikar kafa kasar Yoruba a karkashin umarnin shugabansu wanda aka bayyana da Black Lion, sun yi yunkurin kwace gidan rediyon Amuludun FM radio wanda ke Ibadan ta hanyar amfani da karfi a ranar Lahadi.

Masu fafutikar sun kutsa cikin gidan rediyon gwamnatin tarayyar ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi inda suka kwace wayoyin hannun ma'aikata tare da shelanta kafa kasar Yoruba tare da ficewa daga Nijeriya.

Sai dai biyar daga cikin masu fafutikar 'yan sanda sun kama su.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adebowole Williams, ya nuna wadanda ake zargin a cibiyar hukumar 'yan sandan ta Eyeleye da ke Ibadan a ranar Lahadi.

Williams ya bayyana cewa jami'an hukumar na gudanar da sintirin tattara bayanai ne lokacin da suka samu kiran neman taimako cewa mambobin wata kungiya da ke da niyyar warewa, ta hanyar karfi sun kutsa cikin gidan rediyon Amuludun 99.1 FM da ke Moniya a Ibadan da niyyar ayyana ficewarsu daga Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.

'Yan sandan nan-da-nan suka dauki mataki a kan ka'ida domin aikin yin ceto tare da kama wadanda ake zargi.

Williams ya tabbatar da cewa ba wani jami'i ko kuma wani mutum daban da aka raunata sakamakon al'amarin.

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa ya shaidawa wata kungiyar bincike, karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da shiyyar binciken manyan laifuffuka na jihar, da su samar da bayani game da duk wani abu da ya shafi al'amarin.

An ma nemi kungiyar binciken da ta fadada kamen da ta ke yi ta hanyar gudanar da bincike a hankali.

Ya dai bayyana wannan al'amari a matsayin laifi, rashin kashin kasa ne kuma a fili aikin ta'addanci ne wanda za a hana afkuwarsa a karkashin dokar kasa.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya bayyana cewa wani ne wanda aka fi sani da Black Lion ya ba su umarnin su kwace tashar su kuma watsa cewa an kafa kasar Yoruba kuma ba bu abinda 'yan sanda ko sojojin Nijeriya za su iya yi masu.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa mutumin da ya ba su umarnin ba a Nijeriya ya ke zaune ba kuma cewa sun tuntube shi ne ta hanyar kiran waya.

Ya kara da cewa ba a yi masu alkawarin kudi ba kafin su aiwatar da al'amarin, inda ya kara da cewa ya zo Ibadan ne a ranar Juma'a daga Enugu inda ya ke zaune domin yin wannan abu.

No comments

Powered by Blogger.