Majalisar Isra'ila ta Knesset na neman kafa dokar hana nuna tutar Falasdinawa a bainar jama'a
'Yan majalisar kasar Isra'ila na neman tabbatar da wani kuduri wanda zai sa hukuncin nuna tutar Falasdinawa ya kasance na zama a kurkuku na kusan shekara daya a cikin wani yunkurin musgunawa daga gwamnatin ta Isra'ila wadda Firaministan Benjamin Netanyahu ke jagoranta.
Dokar na samun goyon baya daga mambobin majalisar masu tsatstsauran ra'ayi na jam'iyyar Jewish Party, ta ma bayyana cewa mutane biyu ko uku in sun kada tutar abinda suka kira "wasu mutane da ba a shiri da su" za a dauki haduwar mutanen abinda ya ke haramtacce kuma wanda zai haifar da yin hukunci.
Tuni dai majalisar ta Isra'ila ta Knesset ta kada kuri'a kan amincewa da kudirin a matakin farko, kuma kudurin na bukatar wasu kuri'un uku kafin zama doka.
Tun dai fara mulkin su a matsayin mulkin da ya fi goyon bayan tsarin gurguzu a tarihin Isra'ila, majalisar Netanyahu ta kirkiro kudurori wadanda za su faranta ran al'ummar da ke da tsatstsauran ra'ayi a yankunan da aka mamaye.
Shirin rage karfin kotun kolin kasar ya fusata yahudawa 'yan kama-wuri-zauna wadanda ke kallon hakan a matsayin hari kan tsarin tabbatar da bincike da kuma adalcin su. Dokar tuni ta haifar da zanga-zanga ta watanni a yankunan da aka mamaye tun farkon wannan shekarar.
To sai dai kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Hamas wadda ke Gaza ta ji labarin shirin majalisar ta Isra'ila na hana tutocin Falasdinawa a bainar jama'a, inda ta bayyana cewa wannan na cikin yaki kan addini wanda gwamnatin masu tsatstsauran ra'ayi ta kaddamar a kan Falasdinawa.
"Amincewa da wannan kudurin dokar ta hanyar karanta sa a majalisa zai ba jami'an tsaron Isra'ila damar kara take hakkin mutanen Falasdinu." Kamar yadda jawabin ya bayyana a ranar Alhamis.
Ya kara da bayyana cewa irin wannan matakin ba zai ba Falasdinawa tsoro ba ko hana su kada tutar kasarsu wadda ke yin nuni da alamin su, hadin kan su da kuma yunkurin su.
Hamas ta cigaba inda ta yi kira ga kasashen duniya, majalisar dinkin duniya da duk wasu kungiyoyi da suka damu da al'amarin da su yi Allah wadai da tsare-tsaren Isra'ila da laifuffukan ta, wadanda sun keta manyan hakkoki da tsarin hakkokin bil-adama.
Kungiyar fafutikar ta nemi majalisun duniya da su goyi bayan Falasdinawa a yunkurin su na hadewa da kuma samun 'yanci.
Post a Comment