Header Ads

Yahudawa a Isra'ila sun kutsa harabar masallacin al-Aqsa kafin su yi "zagayen daga tutoci" domin tunawa da mamayar da Isra'ila ta yi a 1967

Wasu yahudawan Isra'ila 'yan kama-wuri-zauna da suka kutso cikin harabar masallacin al-Aqsa karkashin kariyar jami'an tsaro

Daruruwan yahudawa a Isra'ila sun kutsa harabar masallacin al-Aqsa, a yayin da aka kawo dubunnan jami'an tsaron Isra'ila birnin mai tsarki domin samar da kariya wajen gudanar da "zagayen daga tutoci" wanda ya kasance wanda zai iya tono rikici.

Kungiyoyi uku na yahudawa 'yan kama-wuri-zauna masu tsatstsauran ra'ayi ne dai suka kutsa harabar masallacin na al-Aqsa a safiyar ranar Alhamis a karkashin kariyar jami'an tsaro masu yawa da kuma tsauraran matakan tsaro na jami'an tsaron Isra'ila, a cikin yahudawan har da malamin yahudawa mai tsatstsauran ra'ayi kuma tsohon mamba a majalisar kasar Isra'ila ta Knesset, Yehudah Glick, kamar yadda wadanda al'amarin ya faru kan idanunsu suka bayyanawa cibiyar watsa labaru ta Falasdinawa.

Jami'an 'yan sandan Isra'ila kusan 3,000 aka ajiye a wurare daban-daban da ke al-Quds da aka mamaye, an yi shingaye daban-daban a kan manyan tituna wadanda suka hana yin al'amurran rayuwa daban-daban kamar yadda aka saba, kafin abinda suka kira zagayen daga tutoci, wanda aka shirya yi da yammacin ranar Alhamis.

An ma bayar da umarnin a kulle shaguna na kwana daya domin yahudawa 'yan kama-wuri-zauna su samu shiga tsohon birnin ba tare da wahala ba.

Ana dai sa ran zagayen zai bi ta wajen Bab al-Amoud ne wanda aka san shi da Damascus Gate, wani yanki na musulmai da ke tsohon birnin al-Quds kafin daga bisani zagayen ya je Western Wall plaza.

'Yan majalisa masu tsatstsauran ra'ayi da ministoci, ciki harda Itamar Ben Gvir, sun yi niyyar halartar zagayen.

Zagayen daga tutocin ana yin sa ne a duk shekara domin tuna mamaye gabar yamma da kogin Jordan da kuma al-Quds da Isra'ila ta yi ne a shekarar 1967. Wasu yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ne ke shirya shi a harabar masallacin al-Aqsa da ke al-Quds da aka mamaye.

Zagayen har wa yau yunkuri ne daga wasu yahudawa 'yan kama-wuri-zauna wajen nuna rashin jin dadinsu kan gazawar Tel Aviv wajen hukunta Falasdinawa da kuma tabbatar da kasancewarsu a birnin na Falasdinawa da kuma wuraren shi masu tsarki.

Sai dai kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da wannan al'amari da suka shirya yi, inda ta bayyana cewa, "Zagayen daga tutocin wani yunkuri ne wanda bai yi nasara ba na tabbatar da tsare-tsaren yahudanci na nuna wariya."

Kakakin kungiyar Hamas, Abdel Latif al-Qnoa, ya bayyana cewa kungiyar ba za ta taba barin Isra'ila ta aiwatar da "Shaidanun shirye-shiryen" ta ba na samun iko kan al-Aqsa ta hanyar shirya zagayen wanda ka iya haifar da rikici ko kuma kai hare-hare akai-akai a kan wuri mai tsarki.

Ya bayyana cewa dagewar Isra'ila cewa sai ta yi zagayen ya kamata ya farkar da gaba daya musulmai da al'ummar larabawa. 

Ya ma bayyana a fili cewa shirin Isra'ila na yahudantarwa ba zai canza yanayin musulunci da larabci na masallacin al-Aqsa da kuma al-Quds ba.

No comments

Powered by Blogger.