Atisayen sojoji da Hezbollah ta yi na nuni da cewa ƙungiyar na ƙara ƙarfi a kullum - mai sharhi kan siyasa da doka
Wani Bafalasdine mai fafutika kuma lauya ya bayyana cewa atisayen sojoji da kungiyar fafutika ta Hezbollah da ke Lebanon ta yi a 'yan kwanakin baya na tabbatar da cewa karfin kungiyar na karuwa.
Saleh Abu Izzah, wani sanannen masani dangane da harkokin da suka shafi yammacin Asia, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tattaunawa da kafar watsa labaru ta yanar gizon Press TV a ranar Asabar 27 ga watan Mayu yayin da ya ke bayani a kan babban sakon da aka aikawa gwamnatin Isra'ila ta hanyar gudanar da atisayen sojoji da Hezbollah ta yi a 'yan kwanakin baya.
Kungiyar ta gudanar da wani babban atisayen sojoji ne a kudancin kasar Lebanon a ranar wata Lahadi a cikin watan Mayu, kafin gudanar da tunawa da kwace yankin karo na 23 daga hannun mai mamaya Isra'ila.
Atisayen wanda aka yi a kusa da sansanin kungiyar da ke kusa da kauyen Mleeta a kudancin Lebanon, ya hada da hare-hare da dama da ke nuni da hare-haren Hezbollah a kan wuraren Isra'ila da dama a duk wani yaki da ke iya faruwa a nan gaba.
Kungiyar ta ma nuna karfin yakin ta, yayin da mayakan ta suka gudanar da fareti a cikin motoci da kan mashina.
"Sakon da Hezbollah ta aika daidai ya ke kuma kai tsaye. Ina nufin ta tabbatar da cewa tana da karfi kuma ta shirya." Kamar yadda mai sharhin ya bayyana.
Abu Izzah ya bayyana cewa ta hanyar atisayen sojojin ta, Hezbollah ta nuna ba wai kawai za ta iya kawar da kowanne kutse na Isra'ila ba ne, amma za ma ta iya sake kwato wurare tare da shimfida ikon ta har zuwa yankin al-Jalil da ke yankin arewacin wuraren da Isra'ila ta mamaye.
Ya ce sashen tsaron Isra'ila da sojojin Isra'ila da 'yan siyasar ta sun sami sakon Hezbollah a matakai guda uku.
"Na farko sun gane cewa Hezbollah na da karfi, kuma karfin ta ba tsaye ya ke cak ba, yana karuwa ne a kullum. Kuma, irin ilimin da kungiyar ta samu yayin yakin Siriya ya kara karfin sojojin kasan ta ba kadan ba." Abu Izzah ya bayyana.
"Na biyu (atisayen) ya nuna cewa Isra'ila ba ta da karfin tunkarar Hezbollah kuma kungiyar tana cigaba da yi wa gwamnatin barazanar da ba ta taba tunani ba."
"Na uku, matakin da kawai Isra'ila za ta iya dauka kan Hezbollah shine na farfagandar kafafen sadarwa da nuna fin karfi. Amma barazanar ta ba za ta iya fitowa fili ba kuma ba za ta iya haifar da wani abu kan Hezbollah ba a kan kasar Lebanon." Mai sharhin ya bayyana.
Sai kuma ya tabo bangaren Netanyahu kan shirin sa na rage karfin sashen shari'a, wanda ya haifar da zanga-zangar satuttuka a cikin watanni biyar da suka gabata wanda kuma 'yan adawar Firaministan na Isra'ila suma suka nuna kin amincewarsu.
Abu Izzah ya ce Netanyahu ya kirkiro tsarin ne bayan Isra'ila ta kasa yin nasara a yakin kwanaki biyar da ta yi a zirin Gaza, wanda ya samar da nasara ga Islamic Jihad da kuma sauran kungoyoyin fafutika.
Ruwan makamai masu linzami na Falasdinawa a kan biranen Isra'ila da gine-ginen ta, a abinda suka kira da "Daukar fansar masu 'yanci" ya kara nuna rashin karfin Isra'ila in an kwatanta da kungiyar fafutikar.
Mai sharhin ya bayyana cewa Netanyahu na tunanin cewa shirin rage karfin sashen shari'ar hanya ce mai kyau ta ruruta gabadaya yadda al'amurra suke a Isra'ila domin ya dogara a kan hauhawar rarraba a tsakanin magoya bayan hadakarsa ta tsatstsauran ra'ayi da kuma 'yan adawa.
Da aka tambaye shi ko Netanyahu zai iya tunkarar baki daya kungiyoyin fafutikar Falasdinawa tare da mayar da rigimar da ke fuskantar majalisar sa zuwa wajen yankunan da aka mamaye, sai Abu Izzah ya ce in an yi la'akari da rikicin baya-bayan nan da kungiyoyin fafutikar Falasdinawa, Netanyahu ba zai iya yin hakan ba.
"Shi (Netanyahu) ba zai iya kare Tel Aviv ba daga makamai masu linzamin Islamic Jihad, ta yaya kuma zai iya fara yaki da Iran ko Hezbollah?" Kamar yadda ya bayyana.
Zai iya kasancewa Netanyahu ya kara yawan tursasawarsa kan mayaka masu fafutika da ke yamma da gabar kogin Jordan da kuma al-Quds, ciki har da sabbin gine-gine da ayyukan soji a kan masu fafutika, domin canza yadda al'amurra suke a kasa da kuma samun goyon bayan yahudawa yan-kama-wuri-zauna.
"Amma, fara sabon yaki a zirin Gaza da kuma wani wurin da ba (gabar) zirin ba zai kasance aikin kawai da kuma wani al'amari da ba zai yi nasara ba." Cewar Abu Izzah.
Post a Comment