Ƙungiyar ma'aikatan tashoshin jiragen ruwa ta fara yajin aiki, ta kulle duk tashoshin jiragen ruwa da ke faɗin ƙasa
Ƙungiyar ma'aikatan tashoshin jiragen ruwa ta Nijeriya (MWUN) da safiyar ranar Litinin ta fara yajin aiki na kasa baki daya sakamakon wasu al'amurra da ba a warware su ba da suka shafi rashin kulawa da mambobinta yadda ya kamata.
Ma'aikatan a ranar Litinin sun yi zanga-zanga a Legas dauke da alluna da ke dauke da bayanin dalilin da ya sa suka fara yajin aikin tare da neman bukatunsu daga gwamnatin Nijeriya.
"Muna so a sake yin duba ga garatutin ma'aikatan jiragen ruwa." Kamar yadda ya ke a rubuce a jikin wani allo.
A ranar Alhamis da ta gabata, kafar watsa labaru ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa shugaban kungiyar ta MWUN, Prince Adewale Adeyanju, yayin wani taron manema labaru, ya bukaci duka mambobinsa su shiryawa yajin aiki a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa duk da jawabai na karshe da aka cimmawa, kamfanonin jiragen ruwa sun ki samar da cigaba ga yanayin jin dadin ma'aikata.
Ya koka da cewa ma'aikata a masana'antar jiragen ruwa ana daukar su kamar bayi.
A cikin watan Fabrairun shekarar 2022, kungiyar ta taba tafiya yajin aiki na kwanaki 14 sakamakon rashin bin dokokin da kamfanonin mai na kasa-da-kasa suka yi na dokar da shafi masu dorawa da sauke kayayyaki daga jirgi mai suna "Extant Stevedoring Regulations" wadda aka fi sani da "Government Marine Notice 106" ta shekarar 2014.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa kamfanonin man na kasa-da-kasa, IOCs, sun ki kyale kamfanonin da ke saukewa da dora kayayyaki isa wurarensu domin fara aiki, hana ma'aikatan da ke saukewa da dora kayayyaki wadanda aka yiwa rijista da kuma kamfanonin da ke saukewa da dora kayayyaki yin aiki a wuraren IOCs din kamar yadda doka ta tanada.
Post a Comment