Header Ads

'Yan ta'adda sun sace 'yan mata 30, sun kashe da dama a wasu al'ummu na jihar Zamfara

'Yan ta'adda sun sace matan da ba su gaza 30 ba tare da kashe da dama a yayin da suka kai hari a wasu al'ummu da ke karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara.

Kamar yadda kafar watsa labarun Chronicle ta ruwaito, 'yan ta'addan sun kashe 'yan kauye sama da mutum 20 tare da raunata wasu yayin da suka kai hari al'ummun Sakkida da Janbako da ke jihar.

A cikin wata hira a ranar Lahadi, wani wanda ya tsira ya shaidawa kafar watsa labaru ta BBC Hausa cewa wata daga cikin 'yan matan da aka sace da ta samu ta gudo daga wajensu ta dawo da dankwalinta ne kawai.

Wani mazaunin kauye da ya tsira daga harin ya bayyana cewa, "Mun farka cikin zaman lafiya, an yi ruwan sama kuma wasu mazauna kauye sun shirya domin tafiya gona. Kwatsam, sai muka ji cewa wasu 'yan ta'adda sun kai hari wani kauye da ke makwaftaka da mu, Sakkida.

"Jami'an bijilanti da ke kauye, JTF sai suka yi kira ga mutanen Janbako suna neman taimako. Wadanda suka sadaukar daga wajenmu da sauran mutanen al'ummarmu sai suka dauki makamai suka tafi kauyen.

"Akwai wani tsauni kafin ka kai kauyen. Ba su san cewa 'yan ta'addan sun yi kwantan bauna ba, sai suka bude wuta a kan mutanenmu. A yau a Janbako, mutane 22 aka bizne.

"An kira jami'an tsaro amma sun bayyana cewa ba za su samu zuwa ba nan-da-nan domin motar da ke kwaso jami'ansu ba ta nan. Hilux ce kawai suke da ita. Jami'an tsaron sun yi kokari, sun kori 'yan ta'addan. Lokacin da suka dawo, sun dawo da mashinan da suke mallakin 'yan ta'addan.

"Mutane da yawa sun raunata, wasu an harbe su, wasu an sare su. A Janbako babu wani jami'in tsaro da aka ajiye domin samar da tsaro." Kamar yadda ya bayyana.

Wani mazaunin kauye ya shaidawa manema labaru cewa an sace 'yan mata a kauyen Gora yayin da suke samo iccen girki a cikin daji a Daggera, inda ya kara da cewa ko a satin da ya gabata ma 'yan ta'addan sun kashe mutum uku tare da sace wasu uku.

"Yanzu sun sace 'yan matanmu, sama da 30, sun turo sako cewa a wannan shekarar in muna so mu noma gonakinmu a Daggera sai mun yi yarjejeniya da su. Dama muna yin hakan da su, ba za mu iya kirga yawan yarjejeniyar da muka shiga ba. Ba mu san abinda za mu yi ba." Kamar yadda ya bayyana

Ya bayyana cewa an sace 'yan matan ne da tsakar ranar Asabar, kuma an ga daya daga cikinsu tana gudu ta dawo da dankwalin kan ta kawai.

Ya yi ikirarin cewa jami'an tsaron sun kasa kamowa tare da dawo da 'yan matan da aka sace na jihar Zamfara.

Kafar watsa labaru ta BBC Hausa ta ruwaito cewa 'yan sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da faruwar al'amarin amma ba su bayar da cikakken bayani ba.

No comments

Powered by Blogger.