Dalilin da ya sa muka kutsa ginin da EFCC ke amfani da shi a Legas, barin ma'aikatansu a waje - Hukumar DSS
Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, DSS, ta tabbatar da cewa jami'an ta sun kama iko da ofisoshin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ke amfani da su a jihar Legas a ranar Talata tare da bayyana cewa ita (DSS) ce ke da mallakin wajen a ka'ida kuma "ta kawai shiga wurin da ya ke na ta ne."
Dama kafin nan, kafar watsa labaru ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa jami'an na DSS sun afka ofishoshin hukumar ta EFCC wanda hakan ya hana jami'an hukumar iya shiga ofisoshin na su da ke Ikoyi a jihar Legas.
Kwararan majiyoyi daga duka hukumomin biyu sun tabbatar da cewa akwai rashin jituwa da ke cigaba da wakana a tsakanin DSS da EFCC din kan mallakar ginin.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar ta DSS sun afka ofishin ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Talata tare kuma da kin fita da ofishin duk da sasantawar da aka yi a tsakanin jami'an hukumomin biyu.
Yayin da ta ke magana a kan al'amarin, hukumar EFCC a cikin wani jawabi ta bakin kakakin ta, Wilson Uwujaren, ta bayyana kutsawar da abun ban mamaki, inda ta bayyana cewa hakan zai shafi yakin da ake yi a Nijeriya kan laifuffukan da suka shafi kudi da tattalin arziki.
Sai dai hukumar ta DSS a cikin wani jawabi ta bakin jami'in ta mai kula da hulda da jama'a, Peter Afunanya, ta musanta cewa ta killace ofishin na EFCC ta kuma musanta cewa ta hana jami'anta shiga, inda ta bayyana cewa hukumar ba fada ta ke yi da EFCC kan ginin ba.
A cikin wani jawabi da DSS din ta fitar, ta bayyana cewa, "Hankulanmu sun karkato kan rahotannin wasu kafafen watsa labaru da ke cewa DSS ta hana hukumar EFCC shiga ofishinta da ke Legas.
"Ba daidai ba ne wai DSS ta hana EFFC shiga ofishin ta. A'a, ba gaskiya ba ne. Hukumar ta shiga ofishin ta ne kawai inda ta ke yin ayyukanta da gudanar da nauyin da ya hau kan ta a doka.
"Amma ba bu wata gardama dangane da No 15 A Awolowo Road kamar yadda kafofin watsa labaru ke fadi. EFCC sun fada maku suna nema su kasance su ke da iko da ginin? Zan yi mamaki idan suna so su kasance su ke da mallakin ginin.
"Awolowo Road cibiya ce ta NSO. DSS/SSS ta fara ne daga nan. Wannan wani abu ne da kowa ya sani. A tarihi haka ya ke. Ku duba ku gani.
"Ba wata rashin jituwa a tsakanin DSS da hukumar EFCC a kan wani abu. Ina neman ku da kada ku kirkiro wani. Su manyan abokai ne wadanda ke aiki domin nasarar kasa. Kada ku yarda da duk wani bayanin fada."
Post a Comment