Header Ads

Sojojin Sudan sun dakatar da kasancewar su a cikin tattaunawar tsagaita wuta

Shugaban sojojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan

Sojojin Sudan sun dakatar da kasancewarsu a cikin tattaunawar da ke samun goyon bayan Saudiyya da dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF).

Duk da yunkurin samar da zaman lafiya, fada ya cigaba da kasancewa a kasar ta nahiyar Afirka a ranar Laraba, inda sojojin da RSF suka rinka dora tuhuma a kan juna kan keta ka'idojin tsagaita wutar.

Birgediya Nabil Abdallah, kakakin sojojin, ya bayyana cewa an dauki matakin ne sakamakon keta ka'idojin tsagaita wutar akai-akai da RSF ke yi.

Ya bayyana cewa RFS ta ma ki tabbatar da neman da aka yi gare ta na ta janye daga cikin asibitoci da gidaje.

Sai dai RSF din ta zargi sojojin da tsayar da tattaunawar da ake yi a birnin Saudiyya na Jeddah domin ta yi mata illa da kuma keta ka'idojin tsagaita wutar ta hanyar yin amfani da karfin hare-haren sama da manyan bindigogi domin kai hari ga wuraren ta.

Majalisar kasashen Afirka (AU) da yammacin ranar Laraba ta ce dakatawa da tattaunawar ka da ya sa rashin kwarin gwiwar shiga tsakani. 

"A sansantawa da ke da wahala, dama wani al'amari ne da aka saba gani wani bangare ya dakata ko ya yi barazanar dakatawarsa" a ciki, Mohamed El Hacen Lebatt, shugaban ma'aikatan hukumar AU ya bayyana, kuma kakakin ta a rikicin Sudan.

"To amma kada wannan ya sa rashin kwarin gwiwa ga masu shiga tsakani... Amurka da Saudiyya, wadanda mu ke goyon baya sosai, daga cigaba da kokarinsu." 

Zuwa yammacin ranar Talata, an ruwaito arangama mai karfi a Khartoum, inda mazauna suka ruwaito an yi fada mai karfi a duka bangarori uku da suka hada babban birnin a kusa da rafin Nile - Khartoum, Omdurman da Khartoum ta Arewa.

Yankunan babban birnin sun fuskanci kwashe kayayyakin da ke cikinsu da daukewar wutar lantarki da ruwa akai-akai. Mafiyawancin asibitoci ba su aiki.

Wasu hukumomin samar da agaji, ofisoshin jakadanci da kuma bangaren gwamnatin Sudan ta tsakiya sun mayar da ayyukansu zuwa Port Sudan, jihar Sudan da ke kusa da tekun Red Sea, inda nan ne babban wurin sufurin jiragen ruwa kuma inda ya fuskanci rikici amma kadan. 

Wannan al'amarin da ke faruwa yanzu yana zuwa ne bayan Amurka da Saudi Arabiya da ke shiga tsakani sun bayyana cewa bangarorin da ke fada da juna sun amince su kara wa'adin yarjejeniyar tsagaita wutar zuwa wasu kwanaki biyar.

Yakin dai ya tilastawa mutane kusan miliyan 1.4 barin muhallansu, ciki har da wasu sama da 350,000 da suka ketare iyakar kasar zuwa kasashe makwafta. 

A cikin sati na shida kenan ake a cikin rikici, majalisar dinkin duniya ta yi kididdigar cewa sama da rabin mutanen kasar na bukatar agaji da kariya.

Shugabannin sojoji da na RSF sune ke rike da manyan mukamai a cikin majalisar mulkin Sudan tun bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar, Omar al-Bashir, yayin sanannen boren da aka yi a shekarar 2019.

No comments

Powered by Blogger.