Header Ads

Jirgin ƙarƙashin ruwa na OceanGate da ke ɗauke da 'yan yawon buɗe ido ya fashe

Jirgin karkashin ruwa da ke dauke da fasinjojin biyar 

Masu aikin ceto na cigaba da neman wani jirgin karkashin ruwa da ya bace a ranar Talata, kwana biyu bayan an rasa sadarwa da jirgin wanda ke dauke da 'yan yawan bude ido masu arziki da ke son ganin jirgin Titanic da ya yi hadari a karkashin teku kusa da gabar ruwan kasar Kanada.

Direba daya da fasinjoji hudu ne ke cikin jirgin na karkashin ruwa da ya bace a ranar Lahadi. Wadanda suka kera jirgin sun ce zai iya kasancewa a karkashin ruwa har na tsawon awowi 96 - wanda hakan ke nufin wadanda ke ciki za su iya kaiwa ranar Alhamis kafin iskar da ke ciki ta kare.

Mai aikin tsaron gabar ruwan Amurka, Rear Admiral John Mauger, a cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin ya bayyana cewa masu aikin ceto na cigaba da kokari tsawon dare suna fadada binciken su zuwa can karkashin ruwa, inda ya kara da cewa hukumomi sun fi mayar da hankali a yankin da jirgin ke aiki.

Wadanda ke cikin jirgin na karkashin ruwa, wanda kudin tafiya ga mutum daya a cikinsa ya ke dalar Amurka 250,000, sun hada da biloniya dan kasar Birtaniya Harmish Harding, dan kasuwar kasar Pakistan, Shahzadah Dawood da dansa Suleman.

Mai bincike dan kasar Faransa mai shekaru 77 Paul-Henri Nargeolet da Stockton Rush wanda shine mamallaki kuma shugaban kamfanin jirgin karkashin ruwan da ke Amurka na OceanGate, duk suna cikin jirgin karkashin ruwan kamar yadda kafar watsa labarai ta The Guardian Nigeria News ta ruwaito. 

Jiragen ruwa da jiragen saman Amurka da na Kanada na kaiwa da komowa a yankin. Masu aikin ceto na fuskantar kalubale na neman jirgin karkashin ruwan da kuma mutanen da ke ciki, kamar yadda kwararru suka bayyana.

No comments

Powered by Blogger.