Header Ads

Majalisar ɗinkin duniya ta ware dala miliyan 20 domin haɓaka samar da isasshen abinci a Nijeriya

Majalisar dinkin duniya (UN) ta ware dala miliyan 20 domin cikin gaggawa a fuskanci hauhawar rashin abinci da ingancin abincin a arewa-maso-gabashin Nijeriya.

Mataimakin kakakin majalisar, Farhan Haq, ne ya bayyana haka a yayin wani taron manema labaru a cibiyar majalisar da ke New York.

"Da miliyan tara daga cibiyar samar da kudade na gaggawa (CERF) da kuma dala miliyan 11 daga kudaden ayyukan jin kai na Nijeriya, za mu taimaki yunkurin da gwamnati ke jagoranta a fadin jihohin Borno, Adamawa da Yobe. 

"Taimakon zai hada da samar da abincin da za a iya ci nan take, samun ruwa mai tsafta, kula da lafiya da kuma taimakon aikin gona." A cewarsa.

Kamar yadda masu taimakawa aikin agaji suka bayyana, kusan yara sama da 700,000 'yan kasa da shekaru biyar na iya fuskantar rashin abinci da zai iya shafar rayuwar su a yankin kuma sama da mutane rabin miliyan na iya fuskantar rashin abinci da zai bukaci gaggawa a lokacin da ke tsakanin watan Yuni da Agusta, kamar yadda wani rahoto na PM News ya nuna.

Haq ya ce samar da kudaden na gaggawa za su taimaka wajen fuskantar matsalar, amma wadanda ke taimakawa ayyukan jin kai na bukatar fiye da haka domin hana yaduwar yunwa da karancin abinci.

"Taimakon jin kai na dala biliyan 1.3 ga Nijeriya kashi 26 ne kawai aka samar." Kamar yadda ya bayyana.

Da ya ke bayani ga 'yan jaridu a kan Sudan, mataimakin kakakin ya ce kungiyar yin taimakon na cigaba da samar da taimako domin ceton rayuka ga mutane.

Ya ce a ranar Talata, ofishin hadin gwiwa na al'amurran da suka shafi ayyukan jin kai (OCHA) ya jagoranci samar da kayayyakin agaji a cikin motoci 388 zuwa bangarori daban-daban na kasar.

Da ya ke fadin bayani daga hukumar abinci ta duniya (WFP) ya bayyana cewa hukumar ta kai ga mutane sama da miliyan daya ta hanyar samar da abinci da ta ke yi na gaggawa a cikin sati shida tun bayan da ta dawo da gudanar da ayyukanta a Sudan.

"Wannan ya hada da kaiwa ga mutane sama da 375,000 a arewa, kudu, gabas da tsakiyar Darfur.

"Mutane na cigaba da neman mafaka daga yakin Sudan a kasashe makwafta. Hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya (UNHCR) ta ce sama da mutane 500,000 a yanzu suka ketara kan iyakar Sudan domin gujewa rikicin.

"Za ku iya ganin haka, a jiya, masu bayar da agaji sun ayyana sama da dala biliyan 1.5 domin fuskantar halin neman taimako da mutane suke ciki a Sudan. 

"A yankin, a wurin taron samar da taimakon wanda majalisar dinkin duniya ta jagoranta, tare da gwamnatocin kasashen Misra, Jamus, Katar, Saudi Arabiya, Majalisar Kasashen Afirka (AU) da kuma Majalisar Kasashen Turai (EU)." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.