Kotu ta ba da umarnin a kama Sufeto Janar na 'yan sanda
Kotun ma'aikata ta kasa da ke zaman ta a Abuja ta bayar da umarnin a kama Sufeto Janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali, da sakataren rundunar, mataimakin Sufeto Janar, AIG Hafeez Inuwa, domin kin bin umarnin kotu.
In dai za a iya tunawa, tun da farko kotun ma'aikatan ta bayar da umarni ga IGP din da ya mayar da wasu jami'an 'yan sanda wadanda suka kammala kwas din 33, 34 da 35 na Police Academy, wadanda aka yiwa ritayar dole. Sai dai kotun ta ce Alkali bai bi umarnin ta ba.
Tun dai ranar 19 ga watan Afirilun shekarar 2022, lokacin da kotun ta yi hukuncin, IGP din da sauran mutanen da aka shigar kara ba su bi umarnin kotun ba.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito, kotun ta bayyana cewa Alkali bai bi umarni ta ba.
An dai bayyana cewa jami'an, wadanda ke cikin damuwa sun je kotun ma'aikatan ne inda suka nemi da ta lalata ritayar da shugaban nasu ya yi masu ta dole, kuma a yayin da ya yi dubi ga karar, Alkalin da ke zama a kotun, Alkali Oyebiola Oyewumi, ya bayar da umarni ga IGP din, hukumar ayyuka ta 'yan sanda da kuma sakataren rundunar da su mayar da jami'an wadanda aka yiwa ritayar ta dole nan take.
Post a Comment