Akalla mutane 100, suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin ruwa a jihar Kwara
Akalla mutane 100, ciki har da wani mahaifin da yaransa 4 suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin ruwa a kauyen Egbu da ke karamar hukumar Pategi a jihar Kwara, kamar yadda kafar watsa labarai ta Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi ta'aziyyarsa ga mutanen Pategi kan wannan mummunan labari na hadarin jirgin ruwa inda ake tsoron gomomin mutane sun rasa rayukansu kuma da dama ba a san inda suke ba.
Kamar yadda Vanguard ta tabbatar, al'amarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da mamatan ke dawowa daga wajen wani bikin aure a makwafcin kauyen Egboti da ke jihar Neja.
An ma bayyana cewa igiyar ruwa ce ta ja jirgin inda ta buga shi da bishiya, wanda hakan ya yi sanadiyyar hatsarin jirgin tare da mutuwar mutane da dama.
Baki daya yankin Egboti ya koma wurin zaman makoki yayin da aka gano gawarwaki da ba su gaza 50 ba zuwa yanzu sakamakon al'amarin.
Majiyoyi a kauyen sun shaidawa kafar Vanguard cewa mamatan sun taso ne daga kauyen Kpada domin kasancewa wajen bikin auren a kauyen Egboti.
Majiyoyin sun sake bayyana cewa jirgin ruwan na dauke ne da fasinjoji sama da 300 wadanda ke dawowa daga wurin bikin auren inda ya yi hadari a kauyen Egbu.
Mutanen da suka bayar da cikakken bayani dangane da al'amarin sun bayyana cewa mutane 69 suka rasa rayukansu daga kauyen Egbu, 36 daga kauyen Gakpan da kuma 4 daga kauyen Kpada da ke karamar hukumar Patigi da ke jihar.
A yayin da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Mista Okasan Ajayi, wanda ya tabbatar da faruwar al'amarin ga kafar watsa labarun a ranar Talata, ya bayyana cewa rundunar 'yan sandan jihar ta tura shugaban 'yan sandan yankin karamar hukumar Patigi domin kara samo bayani dangane da al'amarin.
Ya ce, "Akwai karancin rahoto kan jirgin ruwa da ya yi hadari dauke da mutane kusan 100 a wani kauye a karamar hukumar Patigi da ke jihar." Inda ya kara da cewa, "Zan kara ba ku bayanai sosai da zaran na kara samun bayanai masu yawa."
A cikin wani bayanin ta'aziyya wanda gwamnan ya yi ta bakin babban sakatarensa ta bangaren watsa labaru, Rafiu Ajakaye, ya bayyana cewa, "Gwamna ya damu sosai bayan samun rahoton hadarin jirgin ruwa da ya yi hadari wanda ya hada da mutane da dama musamman mazauna Ebu, Dzakan, Kpada, Kuchalu, da Sampi - duka a Patigi." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin gwamnan a ranar Talata.
"Gwamnan na mika ta'aziyyarsa ga mutanen wannan al'ummu da ma na wasu jihohin. Yana Addu'a Allah Ya ji kan wadanda al'amarin ya shafa.
" Gwamnan a yanzu haka yana bibiyar kokarin ceton rai da ake yi wanda aka fara tun daren ranar Litinin, domin ganin ko za a iya samun wadanda suka tsira. Ya yaba da kokarin Etsu Patigi Alhaji Ibrahim Umar Boloji II da sauran hukumomin karamar hukuma a kokarinsu na tseratar da mutane wadanda ka iya tsira daga hadarin."
Post a Comment