Tinubu ya sa hannu a kudirin dokar bayar da bashi ga dalibai
Shugaban kasar Nijeriya, Bola Tinubu, ya sa hannu domin zamowa doka a kudirin bayar da bashi ga dalubai domin cika alkawarin da ya yi lokacin kamfe.
Kakakin gwamnatin tarayya, Mista Dele Alake, ne ya bayyana haka, inda ya ce za a samar da kudaden ne ga Ma'aikatar Ilimi kuma dalubai ne na manyan makarantu za su iya samun su.
Kudirin bayar da bashin ga dalubai wanda kakakin majalisa ta 9, Femi Gbajabiamila, ya dauki nauyin sa, da ke neman samar da bashin da ba ruwa a cikinsa ga dalubai 'yan kasa, ya wuce karantawa ta uku a majalisar sati biyu da suka gabata.
Dokar na neman samar da damar samun karatu mai zurfi ne ga 'yan kasar Nijeriya ta hanyar samar da bashin da ba ruwa a cikinsa daga "Nigerian Education Loan Fund."
Post a Comment