Kwanaki 40 bayan jirgin su ya yi hatsari, an gano yara huɗu a cikin dajin Amazon da ke Colombia
A ranar 1 ga watan Mayu, wani jirgin sama mai sun Cessna 206 mai dauke da fasinjoji 7 ya yi hatsari a sararin samaniyar kasar Colombia, inda ya fada cikin dajin Amazon. Mutane 3 ciki har da direban jirgin sun mutu, an kuma samu gawarwakinsu, sai dai yara hudu sun bace kamar yadda kafar watsa labarai ta Hindustan News Hub ta ruwaito.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta AFP ta bayyana, bayan hatsarin jirgin saman, sojoji sun gudanar da aikin ceto na tsawon satuttuka wajen neman yaran. A yanzu an gano duka yaran hudu da ransu a cikin sunkurun dajin na Amazon.
Shugaban kasar Colombia, Gustavo Pedro, ya bayyana cewa duka an samu yaran hudu da ransu a dajin Amazon da ya ke daga Caqueta a Colombia zuwa yankin Guaviare. Yayin da ya ke bayani a kan haka a kafar Twitter, shugaban ya rubuta, "Farin cikin kasa baki daya! Yara 4 da suka bace tsawon kwanaki 40 a cikin dazuzzukan Colombia an same su da ransu."
A cikin rubutun da ya yi ya hada da wani hoto na manyan mutane. Wasu daga cikinsu sanye da kayan sojoji, wadanda aka ga suna kula da yaran wadanda ke zaune a kan wata shimfida wadda ruwa ba ya iya ketawa a tsakiyar sunkurin dajin.
Kamar yadda ya ke a cikin rahoton AFP, hatsarin ya faru ne lokacin da jirgin saman na Cessna ke kan hanyarsa ta zuwa San Jose del Guavia, wani birni da ke yankin Araracuara da kuma Guaviare da ke Amazons. An yi imanin cewa injin din jirgin ne ya samu matsala, a dalilin haka kuma ya yi hatsari.
A cikin yaran hudu, daya dan shekaru 13 ne, mai shekara 9 da kuma 4. Abinda ya fi ba da mamaki shine wani yaron da ya tsira watanninsa 12 ne. Kakan yaran, Fidencio Valencia, ya bayyana cewa, " E, duka an gano su, amma ina bukatar in shiga jirgi ko kuma jirgi mai saukar ungulu (Helicopter) domin in dakko su ba da bata lokaci ba." Gawarwakin mutane uku da ke tare da shi - mahaifiyarsa, matukin jirgin da kuma wani dan uwa - duk sojoji sun same su ne a wurin da hatsarin ya faru.
Post a Comment