Header Ads

Amurka ta bayyana cewa za ta sake zuba wasu dala biliyan 2.1 na makamai cikin yaƙin Ukraine

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Sojan Sama na Amurka Birgediya Janar Patrick Ryder

Amurka ta bayyana cewa za ta samar da karin wasu dalar Amurka biliyan 2.1 na makamai domin taimakon Ukraine, wanda hakan ke kara shigar da ita cikin yakin duk da gargadi akai-akai daga Rasha.

Pentagon (Ma'aikatar tsaron Amurka) ta bayyana a ranar Juma'a cewa sabon taimakon kudaden na soji mai cin dogon zango zai hada ne da tsaron sararin samaniya da kayyaykin soja na makaman roka, harsasan bindiga da ba a bayyana yawansu ba da taimakon kudi domin horo da sauran dawainiya.

Sabon taimakon zai hada da samar da kudade domin batirin makami mai linzami na Patriot, na'urar tsaron sararin samaniya na Hawk da makamai masu linzami da kananan jiragen yaki marasa matuka na Puma wadanda za a iya harbawa da hannu.

Ta ma kara da cewa taimakon Amurka din za a samar da shi ne a karkashin shirin taimakon tsaro na Ukraine kuma na da niyyar a yi amfani da shi ne cikin watanni masu zuwa ko ma shekaru domin tabbatar da bukatun makomar tsaron Ukraine a nan gaba. 

Wannan taimako dai na soji na baya-bayan nan ga Kiev na nuna dagewar Washington wajen "taimakon karfin Ukraine a yanzu da kuma kasancewar sojojin Ukraine din da karfinsu da kuma korar mai kutse Rasha a lokaci mai tsawo." Kamar yadda Pentagon ta bayyana.

Kakakin Pentagon, sojan sama na Amurka Birgediya Janar Patrick Ryder ya bayyana a ranar Alhamis cewa sojojin Amurka ba su da wani shiri na samar da sufuri kai tsaye ko wasu taimakon ga wuraren da rushewar dam din Nova Kakhovka ya shafa da ke kan Rafin Dnieper.

Washington ta samar da taimakon tsaro ga Ukraine na sama da dala biliyan 36.7 tun bayan da Rasha ta kaddamar da aikin soji na musamman a kasar a cikin watan Fabrairun 2022.

Duk da cigaba da taimakon Kiev da Washington ke yi, gwamnatin Biden ta bayyana cewa sojojin Amurka ba za su yi yaki da Rasha ba a Ukraine.

Jami'an Rasha sun sha maimaita cewa yin ambaliyar makamai ga Ukraine zai kara ruruta abubuwa ne.

'Yan majalisar Amurka na jam'iyyar Republican sun nuna damuwarsu kan tura kayayyakin soji ga Ukraine.

Wata 'ya majalisar Amurka, Marjorie Taylor Greene ta ce taimakon da Amurka ke yi ga Ukraine na soji "yaki ne a kaikaice" da Amurka ke jagoranta kan Rasha.

Ta bayyana cewa yakin Ukraine ya dora wani nauyi na kudi kan Amurkawa, wadanda tuni suke fama da talauci.

Sai dai 'yar majalisar ta amince da cewa yaki "wata mummunar masana'anta ce mai riba" ga gwamnatin Amurka.

Rasha dai ta fara abinda ta kira "aikin soja na musamman" ne a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, a matsayin wani bangare na tsaron kasa kan kara kusantowa daga gabashi da kawancen da Amurka ke jagoranta na NATO ke yi.

No comments

Powered by Blogger.