Header Ads

Hukumar DSS ta kama gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele

Gwamnan babban bankin Nijeriya da aka dakatar yanzu kuma aka kama, Godwin Emefiele

Gwagwarmayar neman samun 'yanci ta fara ga gwamnan babban bankin Nijeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele. Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (DSS) ta kama shi a ranar Juma'a.

Kamun na zuwa ne lokaci kadan bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele din.

Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, an dakatar da Emefiele ne saboda binciken da ake cigaba da yi a ofishinsa da kuma shirin yin canje-canje ga sashen kudi na kasa.

Kafin dai a dakatar da Emefiele din, hukumar ta DSS a ranar 7 ga watan Disambar 2022 a cikin wata kara mai namba: FHC/ABJ/CS/2255/2022 ta nemi umarnin kotun domin ta kama gwamnan babban bankin na Nijeriya (CBN).

Hukumomin tsaro sun zargi Emefiele da samar da kudi ga ta'addanci, ayyukan da suka shafi cuwa-cuwa da laifukan tattalin arziki da za su iya shafar tsaron kasa.

Sai dai babban Alkalin kotun, Alkali J.T Tsoho, ya ki amincewa da wannan yunkuri.

Kotun ta bayyana cewa irin wannan karar da an hado ta ne da yardar shugaban kasa saboda mummunan shafar tattalin arzikin Nijeriya idan aka kama tare da tsare gwamnan babban bankin.

No comments

Powered by Blogger.