Wani hari da aka kai da wuka a Faransa ya yi sanadiyyar raunata yara da dama
Kananan yara da dama sun raunata a safiyar ranar Alhamis bayan da wani mutum rike da wuka ya kai masu hari a filin wasa da ke wani filin shakatawa a garin French Alpine da ke Annecy.
Shaidun gani da ido sun shaidawa kafofin watsa labarun yankin cewa wani mutum da ya lullube kansa ya kaiwa yaran hari ne yayin da suke wasa, kamar yadda kafar watsa labarai ta Mehr News Agency ta ruwaito.
Nan-da-nan dai aka tura 'yan sanda zuwa wurin da al'amarin ya faru kuma Ministan Cikin Gida na Faransa, Gerald Darmanin, ya bayyana a cikin wani sako da ya tura cewa mutum daya da ake zargi "an kama shi, yabo ga irin hanzari da 'yan sanda suka yi cikin al'amarin."
Motar asibiti ta kwashi yaran wadanda suka raunata zuwa wani asibiti da ke kusa. Wata jaridar da ke yankin, Le Dauphine libere ta bayyana cewa yara shida da wani babban mutum daya ne suka raunata. Akalla uku daga cikin yaran aka ruwaito suna cikin mawuyacin hali.
Rahotanni sun bayyana cewa duka yaran suna da shekaru kamar uku ne kuma suna ajin kananan yara ne (kindergarten) inda suke wasa a filin shakatawa na Jardins de I'Europe lakeside, kamar yadda kafar watsa labaru ta CBS News ta bayyana.
Shugaban 'yan sandan yankin ya bayar da umarni da a zagaye yankin tare da neman mutane da kada su zo kusa. Sojoji sun rufe hanyar isa yankin yayin da kuma 'yan sanda ke yin tambayoyi ga shaidun gani da ido.
Post a Comment