Header Ads

Mummunan tarihin kashe ƙananan yara na Isra'ila "abin kunya ne" ga ƙasashen yamma da ke taimaka mata - Iran

Yara 16 da hare-haren Isra'ila ya kashe a tsakanin ranakun 5 zuwa 7 na watan Agustar 2022. Layan al-Shaer ta rasu ne a ranar 11 ga watan Agusta sakamakon raunukan da ta samu.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Iran ya bayyana cewa mummunan tarihin kashe kananan yara ya kamata ya zama dalilin "abin kunya" ga kasashen yamma da ke taimakawa kasar da ba kan ka'ida ta ke ba.

A cikin wani sako a kafar Twitter a ranar Lahadi, Nasser Kan'ani ya nuna rashin amincewarsa da wani rahoto na duk shekara a kan cin zarafin hakkin bil-adama na yara na majalisar dinkin duniya - da za a fitar a sati mai zuwa - da bai sa Isra'ila a ciki ba.

Rahoton na hakkokin bil-adama na yara ya hada da kashewa, cutarwa, keta mutunci, sace yara, hana su kaiwa ga samun agaji da kuma kai hari a makarantu da asibitoci a yankunan da ke fama da rikici.

Rahoton ya na niyyar lissafo wa ne domin wadanda aka bayyana din su ji kunya kuma hakan ya tursasa su wajen tabbatar da matakan kariya ga yara. Ba a saka Isra'ila a cikin jerin wadanda za su ji kunyar ba ko da cewa Isra'ilan ta kashe yaran Falasdinawa masu yawa, duk da cewa kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun sha nanata bukatar hakan, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

"Abin mamaki ne a ce kasar da ke da tarihin kashe kananan yara 160, tsare yara marasa laifi 600 a cikin gidajensu da marasa lafiya Falasdinawa 600, ciki har da marasa lafiya masu nakasa 30, ba ta cancanci shiga cikin jerin majalisar dinkin duniya na wadanda za a kunyata ba." Kan'ani ya bayyana.


"Wannan kuwa duk da cewa kasar da ke kashe yara ba kunya ta kashe yaran Falasdinawa marasa laifi 26 a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar kawai." Ya kara da cewa. "Mummunan tarihin Isra'ila a wadannan ayyuka ya kamata ya zama dalilin jin kunya ga kasashen yamma da ke taimakawa wannan kasa ta wariya." 

A cikin watannin da suka gabata, hare-haren Isra'ila sun kara hauhawa a birane da garuruwan Falasdinawa. Sakamakon wadannan hare-hare, Falasdinawa masu yawa sun rasa rayukansu an kuma kama da dama.

Mafi yawancin kutsen da Isra'ilan ke yi a Nablus ne da Jenin, inda Isra'ilan ke kokarin hana kafuwar kungiyar fafutikar Falasdinawa a kan kasar ta mamaya.

Tun farkon wannan shekarar, Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 126 a Gabar yamma da kogin Jordan, da al-Quds, ciki har da yara 21 maza da yarinya mace daya. A shekarar da ta gabata ne aka fi samun Falasdinawa da suka rasa rayukansu a cikin shekaru 17, inda mutane 155 aka kashe.

No comments

Powered by Blogger.