Dole lauyoyi su shigo cikin yaƙin kawo ƙarshen rashin adalci, rashawa a Nijeriya - LRG
Wata kungiya da ba ta siyasa ba, Lawyers for Reform Group (LRG) ta yi kira ga lauyoyi a kasar nan da su shiga cikin abinda 'yan kasa ke bukata na yaki da kowanne irin nau'in rashin adalci, rashawa da kuma bukata da ake da ita na su taimakawa marasa karfi a shari'a domin kyautata aikin lauyan, bin dokoki da kuma tababbar da samar da adalci wanda ya ke daidai.
Wannan, kamar yadda kungiyar ta bayyana, ya zama dole in an yi la'akari da halin da kasar ke ciki wanda ke neman lauyoyi da dama su shiga cikin wurare da ke muhimmanci na shari'a, tattalin arziki da shugabanci ta hanyar tabbatar da yin shari'a ta adalci ba tare da bata lokaci ba a Nijeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar a ranar 25 ga watan Yuni, daraktan aikace-aikace kuma sakataren kungiyar, kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) yankin Epe, Aare Oladotun Hassan (Esq) ya ma taya sabbin shugabannin kungiyar lauyoyi a bangaren bukatun kasa da cigaban doka (NBA-SPIDAL) da aka zaba Mr. Aikpoko-Martins, Shugaban zartarwa; Princess Frank Chukwuani, Mataimakiyar shugaba; Funmi Adeogun, Sakatariya; Chinedu Odiegun, Ma'aji; Abdullahi Karaye, Sakataren kudi da kuma Charity Ibezim, Mataimakiyar sakatariya murna.
"Muna taya murna Mr. Aikpoko Martins, shugaban zartarwa. Muna tabbatar masa da samun hadin kan mu domin yaki da rashawa.
"Muna nema lauyoyi da dama su shiga cikin yaki da kowanne irin nau'in rashin adalci, rashawa da bukatar da ake da ita na su taimakawa marasa karfi a fannin shari'a kamar yadda doka ta tanadar domin kuma tsarkake tsarin samar da adalci daidaitacce.
"Halin da ake ciki a kasar nan na neman lauyoyi da dama su shiga cikin bangarori masu muhimmanci na shari'a, tattalin arzuki da shugabanci ta hanyar tabbatar da yin shari'a ta adalci ba tare da bata lokaci ba a Nijeriya.
"LRG za ta hada karfi da sabon shugaban da aka zaba ta kuma yi alkawarin ba za ta yi kasa a gwiwa ba a yayin da ya fara haduwa da muhimman mutane a cikin kungiyar NBA-SPIDAL domin ciyar da kungiyar gaba, za mu kasance a shirye domin hada hannu da yin aiki tare.
"Muna addu'ar samun taimakon Allah da samun karfafawa ga Mr. Aikpoko-Martins domin shugabantar NBA-SPIDAL cikin nasara zuwa ga kasancewa ta samu babban cigaba." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.
Post a Comment