Header Ads

Mayakan Hezbollah sun harbo wani jirgi mara mutuki na Isra'ila da ya yi kutse a kudancin Lebanon

Wani mayakin Hezbollah a tsaye a kusa da jirgi mara matukin na Isra'ila a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni.

Mayakan Hezbollah sun tarbe tare da harbo jirgi mara matuki na Isra'ila wanda ke yawo a sararin samaniyar kudancin Lebanon wanda hakan keta hurumin ta ne a matsayin ta na kasa.

Hezbollah a cikin wani takaitaccen jawabi wanda gidan talabijin da ke amfani da harshen larabci na al-Manar ya nuna, ta bayyana cewa ta harbo jirgin na Isra'ila ne da ya shiga sararin samaniyar Lebanon da yammacin ranar Litinin.

Jawabin ya kara da cewa ta harbo jirgin na Isra'ila ne a yayin da ya ke sararin samaniyar yankin Wadi Aaziyyeh da ke kusa da garin Zibqine, wanda ke a kilomita 103 (mil 64) kudancin babban birnin kasar na Beirut sannan kuma kilomita 4 (mil 2.4) daga bodar da Isra'ila ta mamaye, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

A cikin watan Satumbar 2021, Hezbollah ta bayyana cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki da ya shigo sararin samaniyar Lebanon ta bangaren kwarin Maryamin da ke wajen kudancin garin Yater.

Jirgin na Isra'ila an harbo shi ne da "makaman da suka dace" kamar yadda ya ke a cikin jawabin na Hezbollah a lokacin.

Sai dai, sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa "jirgin fadowa ya yi yayin da ya ke ayyukan da ya saba" kuma cewa al'amarin "ana bincike a cikinsa."

Isra'ila akai-akai ta kan keta hurumin sararin samaniyar Lebanon. Gwamnatin kasar Lebanon, Hezbollah da sojojin majalisar dinkin duniya a Lebanon (UNIFIL) sun sha yin Allah wadai da wuce gona da iri da Isra'ilan kan yi, inda suke fadin cewa a fili ya ke keta kudurin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ne na 1701 da kuma hurumin kasar.

Kudurin, wanda ya samar da tsagaita wuta a yakin da Isra'ila ta kaddamar a Lebanon a cikin shekarar 2006, ya yi kira ga Isra'ila da ta mutunta hurumin kasar Lebanon da kuma mutuncin yankin ta.

No comments

Powered by Blogger.