Header Ads

Maciji ya kashe wani kwamandan kungiyar ISWAP a jihar Borno

Maciji

Wani kwamandan kungiyar ISIS a yammacin nahiyar Afirka (ISWAP) ya mutu a jihar Borno 'yan kwanaki bayan maciji ya cije shi. 

Kwararre a bangaren yaki da masu tada kayar baya, Zagazola Makama, ya bayyana cewa kwamandan na ISWAP mai suna Kiriku ya samu raunuka ne a maboyar kungiyar ta ISWAP da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno, kamar yadda kafar watsa labarai ta Trust Radio ta ruwaito.

Kiriku, wanda aka bayyana cewa ya samu raunuka ne a ranar Talata, ya rasu ne a ranar Juma'a.

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana kwamandan na ISWAP bai samu kulawar likitoci ba inda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Kafin rasuwarsa, Kiriku ya aiwatar da abubuwa da dama a yankin Jiddari da ke Chiralia a kusurwar Timbuktu - wani wuri wanda 'yan Boko Haram da kungiyar ta ISWAP ke da karfi.

Kusurwar ta Timbuktu ta hada da kananan hukumomi hudu a jihar Borno - Damboa, Jere, Kaga, Konduga - da kuma karamar hukumar Gujba da ke jihar Yobe.

No comments

Powered by Blogger.