Misra ta fitar da bayanai kan harba tauraron dan Adam na MisrSat 2 da za ta yi kan kuɗi dala miliyan 74
Kasar Misra ta fitar da bayanai kan tauraron dan Adam na MisrSat 2 da za ta harba a kasar Sin a cikin watan Oktoba kan kudi dalar Amurka miliyan 74.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta ruwaito, aikin tauraron dan Adam din shine daukar hotunan kasar Misra domin yin tattalin muhalli da kuma tattaro bayanai dangane da wannan duniyar da kuma sauran duniyoyi (remote sensing).
Dakta Ahmed Al-Rafei, wani jami'i da ke da alhakin gudanar da aikin, ya ce da hadin gwiwar kasar Sin an kammala kafawa da gwada tauraron dan Adam din, inda dalar Amurka miliyan 74 ke zuwa daga Beijing a matsayin abinda ta samar.
An dai shirya cewa MisrSat 2 zai bar Cairo ne a ranar 28 ga watan Yuni domin tafiya kasar Sin inda za a yi masa gwaji na karshe kafin a harba sa.
Hukumar sararin samaniyar kasar Misra ta shirya wani taro domin karbar samfurin kirar tauraron dan Adam din daga kasar Sin.
Taron an yi shi ne a cikin sabon ginin Afirka domin kerawa, gwadawa da ayyukan tauraron dan Adam. Cibiyar kerawa da gwajin tauraron dan Adam ta kasar Misra (AITC) tana da sabbin kayayyakin aiki na zamani a fannin.
Aikin na MisraSat 2 aiki ne na hadin gwiwa a tsakanin hukumar sararin samaniya ta kasar Mirsa da takwararta ta kasar Sin, kamar yadda Al-Rafei ya bayyana.
Kamar yadda hukumar sararin samaniyar kasar Misra ta bayyana, samun fasahar sararin samaniya ga kasar Misra ya zama dole domin ta cimma muradin ta na samun cigaba mai dorewa da cigaban tattalin arziki.
Al-Rafei ya bayyana cewa MisrSat 2 wani cigaba ne a fannin fasahar sararin samaniya, inda ya kara da cewa tauraron dan Adam din wanda ke da nauyin kilogiram 350, yana iya daukar hoto da kyau har na tsawon mita 2 daga kasa a cikin fari da baki da kuma mita 8 mai kala.
Tsawon lokacin da tauraron dan Adam din zai yi a sararin samaniya shine shekara biyar daga lokacin da aka harba shi.
Al-Rafei ya bayyana cewa MisrSat 2 an kera shi ne an kuma gwada shi a aikin gwajin farko da AITC ta yi a cibiyar EGSA.
Kamar yadda EGSA ta bayyana, MisrSat 2 wani abin nunawa ne dangane da hadin gwiwa a aikace a tsakanin kasar Misra da Sin a fannin kere-keren jiragen sama da sararin samaniya a karkashin shirin kasar Sin na habaka safara, sa jari da gine-gine a kasashe da dama (Belt and Road initiative).
An dai kafa EGSA ne a shekarar 2018 domin ta samar, rarrabawa da kuma kawo fasahar sararin samaniya gida ta kuma mallakin karfin da za ta iya kerawa da harba tauraron dan Adam daga kasar Misra, kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta ruwaito.
Post a Comment