Shin gwamna Abba Kabir zai ci gaba da rushe-rushe bayan dakatarwar da kotu ta yi masa?
Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zama a Kano karkashin alkali S.A Amobode ta bayar da umarnin da ba za a jira me dayan bangaren zai ce ba ga gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya dakatar da cigaba da rushe-rushen gine-gine da sauran kadarori a jihar.
Wani dan jihar, Saminu Muhammad, ne ya nemi kotun ta bayar da umarnin ta hanyar lauyansa.
Kotun ta dakatar da gwamnatin jihar da ma'aikatan ta daga rushe wasu gine-gine da ke kan BUK Road kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito.
Alkali S.A Amobode, a bangare guda, ya bayar da umarni ga gwamnatin jihar Kano da ta tsayar da shirin ta na rushe kadarar wanda ya shigar da karar da ke namba 41 da 43 Salanta a kan titin BUK Road da ke Kano.
Wadanda aka hada a cikin karar da aka kai sune Antoni-Janar na jihar Kano, Babban lauyan jihar Kano da kuma hukumar da ke kula da filaye ta jihar Kano.
Sauran wadanda aka shigar karar sun hada da hukumar tsara birane ta jihar Kano, Sufeto Janar na 'yan sanda, rundunar 'yan sandan Nijeriya, kwamishinan 'yan sanda, babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya da kuma hukumar tsaron farin kaya.
Kotun bayan ta saurari karar da wanda ya shigar da karar ya kawo, sai Farfesa Nasiru Aliyu SAN ya bayar da umarnin a gudanar da shari'ar ba tare da bata lokaci ba tare da dage karar zuwa 10 ga watan Yulin shekarar 2023.
Post a Comment