Header Ads

Ministan Isra'ila Ben-Gvir ya yi kira da a "kashe" dubban Falasɗinawa

Ben-Gvir

Ministan Isra'ila mai tsatstsauran ra'ayi, Ben-Gvir, ya yi kira ga majalisa da ta kaddamar da wani babban harin soji a yankin da aka mamaye na Gabar yamma da kogin Jordan, inda ya ke karfafa sojojin kasar da su "kashe daruruwa, in ma akwai bukata, dubunnan" Falasdinawa.

Ben-Gvir ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da kai wurin gine-ginen Evyatar wadanda ba kan ka'ida suke ba da ke saman tsauni a ranar Juma'a, kamar yadda kafar watsa labarai da ke amfani da yaren Hebrew ta bayyana.

Ministan mai ruruta rikici ya kara da bayyana cikakken goyon bayan sa ga yahudawa yan-kama-wuri-zauna tare da kira da a gina gidaje da yawa a Gabar yamma da kogin Jordan.

"A nan, ya kamata a ce akwai cikakkun gidaje, ba ma a nan kawai ba, a duka tsaunukan da ke zagaye." Ya bayyana, inda ya nemi yahudawa yan-kama-wuri-zaunan da su "rugu zuwa saman tsaunukan."

"Ya kamata mu daidaita kasar Isra'ila, a lokaci guda kuma mu kaddamar da aikin soji, mu rusa gine-gine" tare da hallaka ba daya ba ko biyu, amma gomomi ko daruruwa sannan, in kawai bukata, dubunnan Falasdinawa, a cewar Ben-Gvir.

"Saboda, hakan, itace kawai hanya da za mu iya kwace wannan wurin, mu karfafa karfin mu tare da dawo da tsaro ga mazauna." Kamar yadda ya kara da cewa.

Wannan al'amari na zuwa ne a yayin da babban kwamishinan majalisar dinkin duniya a kan hakkokin bil-adama, Volker Turk, ya yi gargadi a farkon ranar cewa yanayin Gabar yamma da Kogin Jordan "na zama wanda ba za a iya shawo kan sa ba" Sakamakon amfani da karfi mai yawa da Isra'ila ke yi da kuma hare-haren da yahudawa yan-kama-wuri-zauna suka kai a cikin 'yan kwanakin nan.

Ya yi kira ga hukumomin Isra'ila da su kawo karshen rikicin nan take su kuma bi dokokin kasa-da-kasa da suka shafi amfani da karfi mai yawa, inda ya bayyana cewa abubuwan da ke haifar da rikicin na Isra'ila da kuma rasa rai a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya kamata a samar masu da mafita cikin gaggawa.

A cikin watannin da suka gabata, hare-haren Isra'ila a kan garuruwa da biranen Falasdinawa sun kara hauhawa. A sakamakon wadannan hare-hare, Falasdinawa da dama sun rasa rayukansu an kuma kama da dama. 

Gwamnatin Tel Aviv ta kara fadada ayyukanta na gine-gine tun cikin watan Disambar da ta gabata lokacin da Benjamin Netanyahu ya dawo kan mulki a matsayin Firaministan majalisar kasar da ta fi kowacce tsatstsauran ra'ayi.

Mafi yawan kasashen duniya suna daukar gine-ginen yahudawa yan-kama-wuri-zauna da ke a yankunan da aka mamaye a matsayin wadanda ba kan ka'ida suke ba.

Sama da yahudawa yan-kama-wuri-zauna 700,000 ke zaune a wurare 230 da aka gina tun bayan mamayar da Isra'ila ta yi a Gabar yamma da kogin Jordan da gabashin al-Quds a shekarar 1967, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

Duka gine-ginen Isra'ila ba kan ka'ida suke ba a dokar kasa-da-kasa. Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da ayyukan gine-ginen Isra'ila a yankunan da aka mamaye a kudururruka da dama.

Falasdinawa na son Gabar yamma da kogin Jordan ya kasance bangaren kasar su mai 'yancin kan ta wadda gabashin al-Quds ne babban birnin ta a nan gaba.

Tattaunawar karshe a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a shekarar 2014 ta rushe. Cikin manyan abubuwan da aka tattauna a kan su a wadannan yarjeniyoyi shine cigaba da fadada gine-gine wadanda ba kan ka'ida suke ba da Isra'ila ke yi.

No comments

Powered by Blogger.