Header Ads

Wata mata ta sace yaro ɗan kwana ɗaya daga asibiti a jihar Legas

Rundunar 'yan sanda a jihar Legas a ranar Juma'a ta kama wata mata mai shekaru 49 kan zargin sace yaro dan kwana daya daga asibiti. 

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamun ga kamfanin dillancin labarun Nijeriya (NAN) a ranar Asabar.

Hundeyin ya bayyana cewa yankin 'yan sandan Ojokoro ne suka yi kamun bayan samun rahoton laifin da misalin karfe 6:00 na yamma.

Ya bayyana cewa rundunar 'yan sandan yankin ta samu bayanin cewa wadda ake zargin ta zo asibitin (wanda ba a bayyana sunan sa ba) da ikirarin cewa ita mara lafiya ce inda ta sace dan karamin yaron.

"Ta shiga bangaren mata inda ta dauki yaron dan kwana daya yayin da mahaifiyarsa ke barci bayan an yi mata tiyata.

"Wata mara lafiya sai ta ga wucewa da sauri na wadda ake zargin da yaro a hannunta, sai ta shaidawa hukumomin asibitin inda aka kama ta.

"Bayan an gudanar da bincike, an gano cewa matar daga jihar Oyo ta ke.

"Matar da ake zargin ta bayyana cewa wani malami ne ya ba ta kwantaragin nemi yaro dan kwana daya domin yin asirin kudi da shi." Kamar yadda ya bayyana.

Hundeyin ya kara da cewa bincike ya nuna wannan shi ne karo na biyu da ake kama wadda ake zargin da satar yaro.

Ya ce yaron an mayar da shi wajen mahaifiyarsa, kuma kakakin rundunar ya bayyana cewa za a yankewa wadda ake zargin hukunci bayan 'yan sanda sun kammala bincike, kamar yadda kafar watsa labarai ta PM news ta ruwaito.

No comments

Powered by Blogger.