Rundunar sojoji ta lalata wuraren tace mai da ba kan ka'ida suke ba 57 tare da kama barayin mai 16
Rundunar sojojin Nijeriya ta lalata wuraren tace mai 57 tare da kama wasu da ake zargin barayin mai ne 16 a cikin sati biyu a yankin Neja Delta.
Rundunar ta ma gano litar danyen mai 122,600, litar AGO 89,850, motoci bakwai, mashinan famfo 18, injin din jirgin ruwa daya, wani jirgin ruwa mai matukar gudu, makamai da ake iya harbawa guda shida daban-daban, wani makami daya da kuma keken uku (tricycle) guda daya.
Daraktan kula da labarun tsaro, Mejo Janar Musa Danmadami, ya bayyana haka a Abuja a ranar Alhamis a wurin taron bayan sati biyu-biyu da ake yi dangane da ayyukan sojojin.
Danmadami ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar iya cigaba da ayyukansu dangane da yakin kan satar mai, wuraren tace mai da ba kan ka'ida suke ba da sauran ayyukan laifuffuka ta hanyar yin kutse mai karfi, sintiri da kuma ayyuka domin tattabar da yadda yanayi ya ke.
Ya bayyana cewa an gano jiragen ruwan katako 27, tankunan ajiya 158, tandoji guda 149 da ramuka takwas wadanda kuma duk an lalata su.
Kamar yadda ya bayyana, duka abubuwa da mutanen da aka kama an mika su zuwa hukumar da ta dace a lokacin domin daukar matakin da ya dace.
"Abu ne mai amfani bayyana cewa an hana kudi naira miliyan 82.4 ga barayin man a cikin lokacin." Kamar yadda ya kara da cewa.
Ya bayyana cewa sashen sojojin na sama a ranar 2 ga watan Yuni da 3 ga watan Yuni sun gabatar da ayyukan bincike ta sararin samaniya da kuma hanawa ta sama a Ngoro Nyong da Ndele wadanda ke cike da ayyukan matatun mai wadanda ba kan ka'ida suke ba.
Ya bayyana cewa wuraren an kai masu hare-hare tare da lalata abubuwan da aka tace din wadanda ba kan ka'ida suke ba kuma kayayyakin aikin sun kama da wuta sakamakon hare-haren jiragen sama.
A kudu maso gabashi, Danmadami ya bayyana cewa rundunar sojojin ta Operation UDO KA na cigaba da takaita ayyukan masu fafutikar kafa kasar Biyafara, 'yan ta'addan Eastern Security Network da kuma sauran laifuffuka a yankin.
Ya bayyana cewa rundunar ta kawar da 'yan ta'adda guda biyu tare da kama wasu da ake zargi mutum 25, tare da samun makamai, makaman da ake harbawa da kuma sauran abubuwa a lokacin.
Post a Comment