Header Ads

Rushe-rushe: Gini ya fado kan masu sace kayayyaki, mutum 2 sun mutu a birnin Kano

Rusau a Daula hotel

Sauran ginin da aka rusa na Daula Hotel da kuma filin Idi a Kano ya ruso a ranar Alhamis, inda ya kashe masu tsince-tsincen kayayyaki a wurin mutum biyu tare da raunata wasu mutum uku.

Babban daraktan hukumar tsara birane a jihar Kano, Alhaji Ibrahim Yakubu, ya tabbatar da da rasuwar masu tsince-tsincen mutum biyu sakamakon rushewar da sauran rusasshen ginin ya yi.

Ginin dai na daya daga cikin gine-ginen da sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rusa.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito, gwamnan na rushe gine-ginen da tsohon gwamnan jihar da ya gada ne ya gina, wandanda ya ke kallo da "ba kan ka'ida ba."

Sai dai Alhaji Yakubu ya bayyana cewa ba za a iya dora laifin rasuwar da samun raunukan da aka yi kan gwamnan ba.

Ya yi mamakin me ya sa mutane ke tsince-tsince a ginin da aka rusa.

Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin jihar na yin rushe-rushen ne da dare domin gudun kada mutane su samu raunuka.

Ya ce sama da shaguna da aka gina ba kan ka'ida ba 1,000 aka rusa a filin Idi.

"Mutane biyu da ke tsince-tsince sun rasa rayukansu, a yayin da wasu da ba su gaza uku ba suka raunata yayin da suke cire kayayyaki kamar roduka, fayef da sauran abubuwa masu amfani daga gine-ginen da aka rushe." Kamar yadda ya bayyana.

Ya bayyana cewa gwamna Abba Yusuf ya yi kira ga 'yan sandan Nijeriya da su tura mutanensu da jami'ansu wuraren da aka rushe domin hana mutane kwasar kayayyaki.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Malam Mohammed Usaini Gumel, ya ziyarci wurin da al'amarin ya faru a ranar Alhamis.

Shugaban 'yan sanda ya gargadi matasa, musamman wadanda ke yin tsince-tsince a wuraren da aka rushe gine-ginen, da ke cin zarafi da kwashe kayayyaki da su daina, domin ba kawai laifi ba ne amma yana barazana ga rayuwa.

"In za a iya tunawa, a ranar 8 da 9 ga watan Yunin 2023, wadanda ake zargi da yin tsince-tsince 106 aka kama tare da tuhumar su da laifuffukan cin zarafi, barna da sata kuma duka an tafi da su kotun Majistire 35 Nomans Land Kano.

"Duk da gargadi da dama na 'yan sandan, masu tsince-tsincen sun ki barin wuraren tare da daina abubuwa a wurin.

"Cikin rashin sa'a, a ranar 15 ga watan Yuni da misalin karfe 2:30 na rana, aka samu rahoton cewa sauran ginin da aka rusa ya fado tare da rufe wasu masu tsince-tsince a Daula Hotel da filin Idi."

Ya yi ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka, inda ya yi kira ga iyaye da sauran shugabannin al'umma da su gargadi 'ya 'yansu su kauracewa wadannan wuraren. 

"Tsaro wani al'amari ne da ya shafi kowa kuma ya kamata a hada hannuwa domin kare rayuka da dukiyoyi." Kamar yadda kara da cewa.

No comments

Powered by Blogger.