Yara miliyan ɗaya sun bar muhallansu sakamakon yaƙin Sudan - UNICEF
Rikicin kasar Sudan ya sa yara sama da miliyan daya sun bar muhallansu ciki har da wasu 270,000 a yankin Darfur, kamar yadda hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana, inda ta ce da yawa na cikin "mummunan hatsari."
Fada na cigaba da faruwa a Sudan tun tsakiyar watan Afirilu tsakanin Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo, wanda ke shugabantar dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF).
Bayan sama da miliyan daya da suka bar muhallansu, akalla yara 330 aka kashe kuma wasu sama da 1,900 suka raunata, kamar yadda UNICEF ta bayyana a ranar Alhamis a cikin wani jawabi, bayan haka "da dama na cikin babban hatsari."
Wakilin hukumar UNICEF a Sudan, Mandeep O'Brien, ya bayyana cewa, "Makomar Sudan abun damuwa ce, kuma ba za mu sa ido muna kallon rasa rayuka da wahalhalu ga yaran ta ba.
"Yara na cikin tsoro da ba sassautawa da firgici, suna fuskantar wahalhalun rikicin da ba su da hannu a ciki - suna cikin wurin da ake musayar wuta, a raunata su, a ci zarafin su, a raba su da muhallansu a kuma sa su fuskanci cututtuka da rashin abinci." Kamar yadda ya bayyana.
UNICEF ta ce a kididdiga yara miliyan 3 ne ke "cikin bukatar" agaji.
Hukumar ta majalisar dinkin duniya ta ce tana a shirye domin ta taimaka masu amma ta yi kira da samun "kariya, rashin wani tsaiko da kuma tabbataccen tsaro domin kaiwa ga duka wuraren da yara ke bukatar taimako."
Ta bayyana cewa yanayin yammacin Darfur - wurin da aka bayyana cewa yara 270,000 sun bar muhallansu sakamakon yakin - musamman nan abin damuwa ne.
"Yanayin da yammaci da kuma tsakiyar Darfur ke ciki, musamman, ana fuskantar fada mai karfi, rashin tsaro mai tsanani da kwashe kayayyakin agaji." Kamar yadda UNICEF din ta bayyana.
"Rashin ruwan sha ya sa dubunnan daruruwan yara cikin hatsarin rashin ruwa a jiki, gudawa da rashin isasshen abinci." Kamar yadda ta bayyana.
A cikin satuttuka da dama, ma'aikatan ceto sun yi gargadin cewa tattalin arzikin kasar Sudan da tsarin kiwon lafiyar ta suna cikin hatsarin rushewa.
Kamar yadda kungiyar likitocin Sudan ta bayyana, kashi uku cikin hudu na asibitocin da ke wuraren da ake fadan ba sa aiki.
Anan tunanin al'amarin zai kara muni sakamakon yanayin damina da ake karatowa wanda zai hana zuwa wasu sassan kasar tare kuma da kara hatsarin cutar maleriya, kwalara da cututtukan da suka shafi ruwa.
Rikicin da ke cigaba da faruwa a kasar Sudan ya yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 2,000, kamar yadda "Armed Conflict Location and Event Data Project" ta bayyana.
Kungiyar shigi-da-fici ta kasa-da-kasa ta bayyana cewa rikicin ya raba mutane miliyan 2.2 da muhallansu, ciki har da 528,000 da suka gudu zuwa kasashe makwafta.
Post a Comment