Header Ads

Gamayyar ƙungiyoyin CSAGP sun nemi Majalisar Dattawa ta sa Tinubu ya cire Minista Matawalle

Ministan tsaro, tsohon Gwamnan Zamfara, Matawalle 

Wata ƙungiya ta gamayyar ƙungiyoyin rajin kare dimokraɗiyya da haƙƙi a ƙarƙashin CSAGP, sun gudanar da zanga-zanga, inda suka yi dafifi a hanyar shiga harabar Majalisar Dattawa, su na neman a cire Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

Premium Times Hausa ta ruwaito cewa masu zanga-zanga na so a cire Matawalle ne dalilin zargin sa da Gwamnatin Zamfara yi kan harƙallar 'sace kuɗaɗe da batun matsalar 'yan bindiga a jihar.'

An dai ga masu zanga-zangar sun je Majalisar Ƙasa inda suka riƙa ɗaga kwalaye a ranar Talata, su na kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya matsa wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu lamba, domin ya tsige Matawalle.

Masu zanga-zangar waɗanda ake kiran gamayyar ƙungiyar ta su da suna 'Civil Society Advocacy Groups and Probity', kuma sun zargi Minista Matawalle da laifin jawo 'yan bindiga a jika, lamarin da suka ce ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da dama a Zamfara da asarar dukiyoyi na biliyoyin nairori.

Gungun 'yan ƙungiyar dai na ƙarƙashin wani mai suna Danesi Momoh, wanda dama tun a wani taron manema labarai a ranar Lahadi ya yi kira da a sauke Karamin Ministan Harkokin Tsaro ɗin.

Matawalle shi ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara wanda Gwamna na yanzu Dauda Lawal ya kayar a zaɓen 2023.

A baya EFCC Ta zargi Matawalle da karkatar da Naira biliyan 70 na gwamnatin Zamfara.

'Yan watanni kaɗan kafin saukar sa daga Gwamnan Zamfara ranar 29 ga Mayu, EFCC ta zargi Matawalle da karkatar da Naira biliyan 70 na al'ummar jihar, lamarin da har ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin sa da shugaban EFCC na lokacin, Abdulrasheed Bawa.

Sai dai kuma shi ma Matawalle ya zargi shugaban EFCC na lokacin, Bawa da neman toshiyar-baki ta dala miliyan 2 a wurin sa. Shi ma Bawa ya ce ƙarya Matawalle ya yi masa.

Masu zanga sun damƙa wa Majalisar Dattawa takardar ƙorafi domin isarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, mai ɗauke da zargin cewa mutum kamar Matawalle ba abin bai wa amanar tsaron ƙasa ba ne, musamman muƙami mai muhimmanci a Ma'aikatar Harkokin Tsaro.

Sun kafa hujjojin su da dalilan su kan wasu zarge-zargen da Gwamantin Zamfara ta watsa kuma ta wallafa, mai nuni kan yadda Matawalle ya karkatar da biliyoyin nairorin Zamfara, a harƙallar kwangiloli daban-daban, ciki har da kwangilar gina filin jirgin saman sauƙale da lodin kaya a Gusau.

Sun kuma tunatar da yadda Matawalle ya ɓoye bargar motocin gwamnati bayan saukar sa daga gwamna.

No comments

Powered by Blogger.