Header Ads

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma'aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba - Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu


Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana a cewa hukumar ta nemi naira biliyan 18 daga kasafin naira tiriliyan 2.17 ne domin ta biya ma'aikatan ta sama da 16,000 kuɗaɗen alawus ɗin da gwamnatin tarayya ta yi masu ƙari a cikin 2023.

Yakubu ya ce ba kamar yadda jama'a ke wa INEC yarfen cewa ta kashe naira biliyan 335 na kasafin 2022 a zaɓen 2023 ba, ya ce naira biliyan 18 da aka ware mata a wannan kasafin ƙarshen 2023, ba a zaɓuɓɓukan gwamnan Bayelsa, Kogi da Imo hukumar za ta kashe su ba.

Da ya ke jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya a ranar Laraba, Yakubu ya ce akasarin kuɗaɗen duk wajen biyan ma'aikata za a kashe su.

Shugaban na INEC ya ce hukumar sa na buƙatar naira biliyan 10.6 domin biyan ma'aikatan ta ƙarin kashi 40% bisa 100% na alawus ɗin da Gwamnatin Tarayya ta yi masu ƙari.

Ya ce INEC na da ma'aikata 16,624.

Ya ce: "Za ku iya tunawa a cikin Afrilu na wannan shekara an yi wa mai'aikatan gwamnatin tarayya ƙarin wasu kuɗaɗen alawus har zuwa kashe 40% bisa 100%. To mu babu wannan ƙarin a cikin kasafin INEC na 2023, saboda an rigaya an rattaba wa kasafin 2023 hannu a majalisa tun cikin Disamba, 2022. A daidai wancan lokacin kuma an fitar da sanarwar daga gwamnatin tarayya a cikin Fabrairu cewa an ƙara wa ma'aikatan gwamnati kashi 40% bisa 100% na alawus ɗin DTA da wasu alawus daban.

"To INEC akwai sama da ma'aikata 15,000. Kuma a yanzu babu yadda za a iya samun kuɗaɗen da za a biya su, idan ba a bijiro da ƙwarya-ƙwaryan kasafin a ƙarshen wannan shekara ba.

"Dalili kenan muka gabatar da buƙatun kuɗaɗen ga gwamnati, don haka aka saka INEC cikin wannan kasafi.

"Kenan INEC ta na buƙatar Naira biliyan 10.6 domin biyan ma'aikatan ta 16,614 alawus ɗin su."

Yakubu ya ci gaba da bayyana yadda hukumar zaɓe ta kashe naira biliyan 355 na cikin kasafin 2022. Ya ce INEC ba ta kashe ilahirin kuɗaɗen kamar yadda wasu mutane ke ta yi wa hukumar yarfe ba.

Ya ce ta yi amfani da wani kaso na kuɗin wajen shirya zaɓen jihar Osun da Ekiti.

Saboda haka sai Yakubu ya ce INEC za ta shirya zaɓen Bayelsa, Imo da sauran kuɗaɗen cikin kasafin naira biliyan 355, waɗanda har yanzu ba su ƙare ba.

Ya ce a yanzu sun nemi Naira biliyan 18 ne daga hannun gwamnati saboda biyan ma'aikata alawus ɗin su, wanda ya yi bayani a baya da kuma ƙarin wasu kuɗaɗe na tilas, musamman saboda yadda aka samu tashin farashin wasu kayayyaki a yanzu cikin 2023, kamar litar fetur, wadda aka yi kasafin kan farashin ta naira 197, yanzu kuma lokacin zaɓuɓɓukan Bayelsa, Imo da Kogi, litar fetur ta haura naira 600.

No comments

Powered by Blogger.