Header Ads

Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama'a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa - Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris a taron da ya yi da manema labarai 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gargaɗin da Amurka ta fitar kan Nijeriya ya na kawo babban cikas ga tattalin arzikin ƙasar.

Idris ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da editocin jaridu a ranar Litinin, a Abuja.

A ranar Juma'a ce, 3 ga Nuwamba, Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar "wata babbar barazana" ga manyan otal-otal da ke faɗin Nijeriya, amma ya ce jami'an tsaron Nijeriya na aiki tuƙuru domin daƙile barazanar.

Idris ya ce, "Abu mafi muhimmanci shi ne kada a yi wa barazana fassarar nuna cewa ta mamaye dukkan faɗin ƙasar nan, domin yin hakan ba wani alheri ba ne."

Ya ƙara da cewa a kullum gwamnati ta na ɗaukar tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a da sauran dukkan maziyarta cikin ƙasar nan da muhimmanci.

Ya ce: "Mun fahimci damuwar da Amurka ke nunawa ko kuma ta nuna a cikin gargaɗin da ta fitar. Amma kuma mun haƙƙaƙe da cewa bai kamata kuma bai dace a nuna wannan barazanar ta shafi dukkan otal-otal ɗin faɗin ƙasar nan ba.

"Abin da mu ka lura shi ne yawancin wannan gargaɗin ba ya haifar da wani alheri, sai dai kawar ya firgita mutane su tashi hankulan su. Sai kuma kawo illa ga tattalin arzikin ƙasa da gargaɗin ke yi. Sannan kuma ya kan zama wata hanyar yi wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samun masu zuba jari a cikin ƙasa zagon ƙasa.

"A kullum mu na bayar da fifiko wajen kare rayuka da lafiyar duk wasu baƙin da su ka kawo ziyara cikin ƙasar nan."

Minista ya ci gaba da bayyana irin nasarorin ga jami'an tsaro su ka samu wajen daƙile matsalar tsaro a wasu jihohin ƙasar nan daban-daban a 'yan kwanakin nan.

No comments

Powered by Blogger.