Header Ads

'Yan Nijeriya za su fara bin diddigin ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa - Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris yayin taron manema labarai 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa kwanan nan 'yan Nijeriya za su samu damar iya bibiya da sa ido kan ayyukan raya ƙasa waɗanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.

Ministan ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da editocin wasu jaridu a ranar Litinin, a Abuja.

A yayin ganawar, Idris ya ce, "Shugaban Ƙasa ya bada umarnin a yi amfani da fasahar zamani domin bai wa 'yan Najeriya damar sa ido, bibiya da bin diddigin ayyukan raya ƙasa waɗanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa a faɗin ƙasar nan.

Idris ya yi kira ga masu kafafen yaɗa labarai da su bayar da goyon bayan wannan tsarin, ta hanyar buga sahihan labarai da yin adalci da sauran su.

Ya ce Gwamnatin Tarayya na ɗaukar dukkan sahihan labarai da muhimmanci domin amfanar dukkan 'yan Nijeriya.

Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta bada damar faɗar albarkacin baki ba tare da dannewa ko tauye haƙƙin kowa ba.

Ya ce: "Ku buga rahoton abin da ya tabbata, ku rabu da dukkan abin da ku ke tababar sahihancin sa, kuma kada ku kasancewa ku na buga labaran da tabbas abin da za ku buga ɗin ya faru.

"Wannan ƙasa tamu ce baki ɗaya, kuma haƙƙin dukkan 'yan Nijeriya su taru su gina ƙasar. Kuma mun san Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ɗan gwagwarmayar dimokiraɗiyya ne da a shirye ma ya ke ya riƙa ba su bayanan duk da ku ka buƙata daga ɓangaren sa." 

Idris ya ce Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na nan na fasalta gagarumin aikin wayar da kan 'yan Nijeriya da za ta yi, ta yadda za a ƙara cusa wa jama'a kishi, ƙaunar ƙasa, haɗin kai da kuma kyawawan ɗabi'u.

No comments

Powered by Blogger.